Acts 8

1Shawul kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa.

Tsanantawa da Warwatsewar Ikkilisiya

A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu koʼina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.
2Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa. 3Amma Shawul ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

Filibus a Samariya

4Waɗanda aka wartsar suka yi ta waʼazin maganar a duk inda suka tafi. 5Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6Saʼad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.

Siman Mai Sihiri

9To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, 10dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” 11Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. 12Amma da suka gaskata da Filibus saʼad da yake waʼazin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. 13Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus koʼina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.

14Saʼad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. 15Da suka iso, sai suka yi musu adduʼa domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, 16domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17Saʼan nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.

18Saʼad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, 19ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yǎ karɓi Ruhu Mai Tsarki.”

20Bitrus ya amsa, ya ce: “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! 21Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi adduʼa ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma ɗaure cikin zunubi.”

24Sai Siman ya amsa, ya ce, “Ku yi adduʼa ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”

25Saʼad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna waʼazin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.

Filibus da Mutumin Itiyofiya

26To wani malaʼikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar-hanyar hamada-da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.” 27Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan maʼajin Kandas, sarauniyar mutanen Itiyofiya. Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada, 28a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan karusarsa yana karatun littafin annabin Ishaya. 29Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin karusan nan ka yi kusa da ita.”

30Sai Filibus ya ruga zuwa wajen karusar ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya, ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”

31Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yǎ hau yǎ zauna tare da shi.

32Bābān yana karanta wannan Nassin:

“An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka,
kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru,
haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.
33A cikin wulakacinnsa aka hana masa gaskiya.
Wa zai iya yin zancen zuriyarsa?
Gama an ɗauke ransa daga duniya.”
Ish 53.7, 8

34Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?” 35Saʼan nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma fada masa labari mai daɗi game da Yesu.

36Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”
Waɗansu rubuce rubucen hannu da suka daɗe suna da baftisma?” 37 Filibus ya ce, “In ka gaskata da dukan zuciyarka, za ka iya.” Bābān ya ce, “Na gaskata cewa Yesu Kiristi shi ne Ɗan Allah.”
37
This verse is empty in this translation.
38Ya kuwa ba da umarni a tsai da karusar. Saʼan nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma. 39Saʼad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki. 40Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana waʼazin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.

Copyright information for HauSRK